wasanni

UEFA ta bai wa Jamus izinin gudanar da EURO 2024

Kasar Jamus ta doke Turkiya a fafutukarsu ta neman izinin karbar bakwancin gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta 2024, wato EURO 2024 bayan kwamitin gudanarwar hukumar ya kada kuri’a.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Jamus, Reinhard Grindel bayan samun izinin gudanar da gasar EURO 2024mbre 2018.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Jamus, Reinhard Grindel bayan samun izinin gudanar da gasar EURO 2024mbre 2018. Fabrice COFFRINI / AFP
Talla

An gudanar da zaman kada kuri’ar ne a birnin Nyon na kasar Switzerland a ranar Alhamis bayan kasashen biyu sun gabatar da yunkurinsu na karshe kan batun.

A karon farko kenan da Jamus za ta gudanar da wannan gasar tun bayan hadewarta da Jamus ta Yamma wadda ta karbi bakwancin gasar a shekarar 1988.

Kawo yanzu, Turkiya ba ta samu damar daukan nauyin wata babbar gasar kwallon kafa ba duk da kokarin da ta yi a shekarun 2008 da 2012 da 2016 na ganin ta karbi bakwancin gasar ta Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI