Wasanni

Morgan ya shawarci Mourinho kan musanya Pogba da Messi

Mai horar da Manchester United Jose Mourinho, da dan wasansa Paul Pogba.
Mai horar da Manchester United Jose Mourinho, da dan wasansa Paul Pogba. REUTERS/Eddie Keogh

Tsohon dan wasan Manchester United, Willie Morgan ya bukaci mai horar da kungiyar Jose Mourinho da ya sayarda dan wasansa mafi tsada Paul Pogba.

Talla

Shawarar ta Morgan ta zo ne, a dai dai lokacinda sabani ke dada bayyana tsakanin mai horar da kungiyar ta Mourinho da Pogba na Faransa, inda rahotannin suka ce an samu musayar zafafan kalamai, tsakanin mai horarwar da dan wasansa yayin gudanar da atasaye.

A cewar Morgan tsohon tauraron Manchester United, muddin Mourinho yana son kawo karshen wannan tsamin dagantaka, ya kuma daidaita al’amuran kungiyar, tilas ya sayar Pogba ya kuma sayo Lionel Messi daga Barcelona, domin maida United kan turbar samun nasarori.

Mourinho dai ya gaza samun nasarar sayan manyan ‘yan wasa, yayin gudanar kasuwar cinikinsu da aka rufe a farkon kakar wasa ta bana, batun da har yanzu ake ce-ce-kuce a kai, a tsakanin wasu ‘yan wasan na Manchester United da ma tsaffin ‘yan wasan kungiyar.

Tsohon dan wasan United Willie Morgan, ya bugawa kungiyar wasanni 236, a tsakanin shekarun 1968 zuwa 1975, inda ya ci mata kwallaye 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.