Wasanni

UEFA za ta soma amfani da fasar taimakawa alkalin wasa

Hukumar kwallon kafa ta kasashen Turai, UEFA, ta ce za’a fara amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da maimaicin bidiyo, a gasar zakarun turai ta kakar 2019/2020, da kuma gasar cin kofin kasashen nahiyar turai da za a yi a shekarar 2020.

UEFA ta amince za ta soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa daga kakar wasa mai zuwa.
UEFA ta amince za ta soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa daga kakar wasa mai zuwa. REUTERS/Jean Pierre Amet
Talla

A cewar hukumar ta UEFA a kakar wasa ta 2020 da 2021, za soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasan, a gasar Europa da kuma ta cin kofin UEFA, wato Super Cup.

Matakin UEFA na amincewar amfani da fasahar maimaicin bidiyon a wasannin da take shiryawa, ya biyo bayan nasarar amfani da fasahar da aka samu yayin gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI