Wasanni

UEFA ta kaddamar da bincike kan Manchester United

Jose Mourinho, mai horar da kungiyar Manchester United.
Jose Mourinho, mai horar da kungiyar Manchester United. Reuters/Jason Cairnduff

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta kaddamar da bincike domin daukar matakin ladabatar da Manchester United, sakamakon rashin mutunta lokaci da kungiyar ta yi, a wasan gasar zakarun turai da ta fafata da Valencia a ranar Laraba.

Talla

‘Yan wasan kungiyar ta United da suka karbi bakuncin Valencia, sun gaza isowa filinsu na Old Trafford akan lokaci, lamarin da ya tilasta, rashin soma wasan na jiya da aka tashe babu ci 0-0, da lattin mintuna biyar.

Hukumar UEFA ta ce sai a ranar 18 ga watan da muke ciki, za ta sanar da hukuncin da za ta yanke kan kungiyar ta Manchester United.

Kafin wannan lokacin dai, mai horar da United Jose Mourinho, ya ce rashin baiwa tawagar ‘yan wasansa rakiyar jami’an ‘yan sanda zuwa filin wasansu kamar yadda aka saba ne ya jawo musu bata lokacin da basu saba ba, inda suka shafe mintuna 45 daga Otal dinsu zuwa fili.

To sai dai rundunar ‘yan sandan birnin Manchester, ta ce ba tada laifi ko kadan, don kuwa ta sanar da United sauyin da aka samu, akan dokar basu rakiya daga masaukinsu zuwa filin wasa, a duk lokacin da zasu fafata, wadda aka janye ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.