Wasanni

Saliyo ta nemi FIFA ta dage mata haramcin shiga wasanni

Shugabar hukumar kwallon kafar kasar Saliyo, Isha Johansen. (12/05/2016)
Shugabar hukumar kwallon kafar kasar Saliyo, Isha Johansen. (12/05/2016) REUTERS/Adrian Dennis/Pool

Kasar Saliyo ta aike da wasika zuwa ga hukumar kwalon kafa ta duniya FIFA, inda take neman hukumar ta janye matakin da ta dauka, na dakatar da ita daga shiga wasanni.

Talla

FIFA ta haramtawa Saliyo shiga wasanni a makon da ya gabata, saboda katsalandan din da gwamnatin kasar ta yi a cikin harkokin hukumar kula da wasan kwallon kafar kasar.

Rikicin cikin gidan ya samo asali ne, bayanda hukumar yakar cin hanci da rashawa ta kasar, ta yi yunkurin sauke Isha Johansen da Christopher Kamara, wato shugabar hukumar kwallon kasar ta Saliyo da kuma sakataren hukumar daga mukamansu, bias zargin sun aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Bayan kamala taron gaggawa a jiya Litinin, tsakanin jami’an hukumar kwallon kafar ta Saliyo da gwamnatin kasar, jami’an kwallon kafar kasar suka aike da wasikar neman FIFA ta dage haramcin wasannin da ta kakaba musu, domin basu damar buga wasa tsakaninsu da Ghana, na neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.