Wasanni

Genoa da Chievo sun kori masu horar da su

Tsohon mai horar da kungiyar Chievo Lorenzo D’Anna
Tsohon mai horar da kungiyar Chievo Lorenzo D’Anna chievoverona.it

Genoa da Chievo, sun zama kungiyoyin a gasar Seria A na farko da suka kori masu horar da su a kakar wasa ta bana, sakamakon jerin rashin nasarorin da suka yi a wasannin da suka fafata kawo yanzu.

Talla

Genoa dake a matsayi na 11 bisa teburin gasar ta Seria A, ta kori kocinta Davide Ballardini, inda ta maye gurbinsa ta tsohon mai horar da ita, Ivan Juric dan kasar Croatia.

A ranar 20 ga watan Oktoba, Genoa za ta yi tattaki zuwa Turin domin fafatawa da masu rike da kofin gasar Seria A Juventus.

Chievo kuwa, wadda ke mataki na karshe a gasar ta Seria A, ta kori kocinta Lorenzo D’Anna, sai dai har kungiyar yanzu bata kai ga bayyana wanda zai maye gurbinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.