Wasanni

Henry na gaf da zama sabon kocin Monaco

Tsohon dan wasan Arsenal kuma mataimakin mai horar da 'yan wasan Belgium a yanzu, Thierry Henry.
Tsohon dan wasan Arsenal kuma mataimakin mai horar da 'yan wasan Belgium a yanzu, Thierry Henry. REUTERS/Sergio Perez/File Photo

Kungiyar Monaco na gaf da bayyana tsohon dan wasan gaba na Arsenal kuma na tawagar kwallon Faransa Thiery Henry a matsayin sabon kocinta.

Talla

Monaco na shirin daukar matakin a kowane lokaci daga yanzu ne, bayan yanke shawarar korar mai horar da ‘yan wasanta, Leonardo Jardim, sakamakon yadda kungiyar ta gaza tabuka abin kirki a gasar League 1 ta Faransa, inda take a matsayin kungiya ta 18 cikin 20.

Tun bayan soma kakar wasa ta bana, wasa guda kawai Monaco ta samu nasara akai, inda ta sha kashi a wasanni hudu, a sauran wasanni guda 10 da kungiyar ta fafata kuwa, ta tashi ne canjaras ko kunnen doki, a ciki da wajen gasar ta League 1 a Faransa.

A baya dai kungiyar Aston Villa dake ingila, ta soma kokarin kulla yarjejeniya da Henry, wanda a halin yanzu ke a matsayin mataimakin mai horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium, Roberto Martinez.

Sai dai wata majiya da ke kusa da tsohon dan wasan na Arsenal ta ce, Henry ya yanke shawarar karbar tayin Monaco da zarar ta gabatar masa da shi, sakamakon shawarar amincewa da hakan, da kocin kwallon kafa na Faransa, Didier Deschamps ya bashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.