Wasanni

Griezmann ya ceto Faransa daga shan kaye a gasar Nations League

Antoine Griezmann na Faransa, yayin murnar jefa kwallo ta farko a ragar Jamus, a wasan gasar Nations League da suka fafata a Faransa.
Antoine Griezmann na Faransa, yayin murnar jefa kwallo ta farko a ragar Jamus, a wasan gasar Nations League da suka fafata a Faransa. REUTERS/Charles Platiau

Antoine Griezmann ya ceto Faransa daga shan kaye a wasan da suka fafata daren ranar Talata tsakaninsu da Jamus, inda Faransa ta samu nasara da kwallaye 2-1, a sabuwar gasar kasashe ta Nations League da hukumar UEFA ta shirya.

Talla

Dan wasan Jamus Toni Kroos ne ya soma jefa kwallo a ragar Faransa, bayan samun damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma daga bisani Grizemann ya zura kwallaye biyu a ragar Jamus.

Griezmann ya ci kwallon farko ne da kai, yayinda ya jefa ta biyu, bayan samun damar bugun daga kai sai tsaron gida.

Har yanzu Faransa bata yi rashin nasara ba a dukkanin wasannin sabuwar gasar ta Nations League da take fafatawa, abinda ya bata damar jan ragamar rukunin farko da take ciki da maki 7, Holland ke biye mata da maki 3 yayinda Jamus ke da maki 1.

A jimlace Faransa bata yi rashin nasara ko da sau daya ba, a dukkanin wasanni 14 da ta fafata a baya bayan nan, ciki harda wasanni bakwan da ta buga na gasar cin kofin duniya ta bana da ta lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.