Wasanni

Rasha ta samu ribar dala biliyan 14 daga gasar cin kofin duniya

Karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ya haifawa tattalin arzikin Rasha da mai idanu.
Karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ya haifawa tattalin arzikin Rasha da mai idanu. REUTERS/Maxim Shemetov

Kwamitin hukumar FIFA da ya lura da shirya gasar cin kofin duniya ta bana, ya ce Rasha mai masaukin baki, ta samu ribar sama da dalar Amurka biliyan 14, sakamakon karbar bakuncin gasar da ta yi.

Talla

Shugaban kwamitin na hukumar ta FIFA da ya jagorancin shirya gasar Alexey Sorokin ne ya bayyana alkalumman a wani taro da suka yi a birnin Doha, domin nazari kan tasirin gasar cin kofin duniyar bana akan tattalin arzikin Rasha.

Kwamitin na FIFA ya kara da cewa gasar cin kofin duniyar ta bada damar samar da sabbin guraben ayyukan yi a Rasha har dubu 315,000, zalika  tattalin arzikin kasar zai ci gaba da amfana sakamakon daukar nauyin gasar, nan da shekaru 5 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.