Wasanni

Messi ba zai buga wasan El Clasico ba

Dan wasan Barcelona Lionel Messi bayan samun rauni a hannu, yayin wasan da suka lallasa Sevilla da kwallye 4-2.
Dan wasan Barcelona Lionel Messi bayan samun rauni a hannu, yayin wasan da suka lallasa Sevilla da kwallye 4-2. REUTERS

Lionel Messi ba zai samu damar buga wasan hammaya na El Clasico da kungiyarsa Barcelona za ta fafata da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid ba.

Talla

Messi ba zai samu buga wasan na El Clasico bane a dalilin raunin da ya samu a wasan gasar La Liga da Barcelona ta lallasa Sevilla da kwallaye 4-2.

Dan wasan na Barcelona ya samu raunin ne, bayan faduwa kan hannunsa na dama da yayi, a lokacin da suke kokarin daukar kwallon tsakaninsa da dan wasan Sevilla Franco Vazquez, hakan ya tilastawa Messi ficewa daga wasan na ranar Asabar ba tare da an kammala ba.

Bayan kammala wasan ne, Barcelona ta bada tabbacin cewa dan wasan nata mai shekaru 31, ya samu dan tsagewar kashi a hannu, dan haka ba zai samu buga wasan El Clasico da Real Madrid ba, zalika ba zai samu buga wasan gasar zakarun turai da Barcelona za ta fafata da Inter Milan ba, cikin wannan mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.