Ronaldo ya kafa sabon tarihi a manyan kungiyoyin Turai
Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa na farko da ya fara cin kwallaye 400 daga cikin wasannin da ya bugawa manyan kungiyoyin nahiyar turai daban daban.
Wallafawa ranar:
Ronaldo ya kafa wannan tarihi ne bayan samun nasarar jefa kwallo guda a ragar Genoa yayin wasan gasar Seria A da suka fafata a jiya, wanda aka tashi kunnen doki, 1-1.
A shekarar 2003 Ronaldo ya sauya sheka daga Sporting Lisbon zuwa Manchester United, inda ya ciwa kungiyar jimillar kwallaye 84 a wasannin Premier League, kafin daga bisani ya koma Real Madrid.
Bayan shafe akalla shekaru 9 tare da Real Madrid, Ronaldo ya ci wa kungiyar kwallaye 311 a wasannin gasar La Liga 292 da ya buga mata.
Daga karshe kuma bayan sauyin sheka zuwa Juventus kan kudi euro miliyan 100 a watan Yulin wanann shekara, zuwa yanzu Ronaldo ya ciwa kungiyar kwallaye biyar a wasanni 9 da ya buga mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu