wasanni

Rangers ta lashe kofin Aiteo bayan doke Kano Pillars

Wasu daga cikin 'yan wasan Rangers
Wasu daga cikin 'yan wasan Rangers premiumtimes

Kungiyar Kwallon Kafa ta Rangers ta nuna bajinta a fafatawarta da Kano Pillars a gasar cin kofin kalubale ta Aiteo Cup, bajintar da ta bai wa masu kallo mamaki.

Talla

Rangers wadda ta lashe kofin gasar, ta rama dukkanin kwallaye 3 da Kano Pillars ta fara zura mata, abin da ya sa a kai ga bugun fanariti har kuma ta samu nasarar daga kofin na bana.

Rabiu Ali da Jimoh Isma’ila na Pillars dukkaninsu sun barar da bugun fanaritinsu, yayin da ‘yan wasan Rangers hudu suka zura nasu fanaritin, abin da ya sa aka tashi wasan 4-2.

An dai gudanar da wasan ne a filin wasa na Stephen Keshi da ke daukar mutane dubu 25 a birnin Asaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.