Wasanni

Cikin fiye da shekaru 10 za a buga El Classico ba Ronaldo da Messi

Kusan dai za a iya cewa wasan zai zama ma'aunin kwazon kowanne Club ba tare da tauraronsa ba, ko da dai dama Madrid na ci gaba da shan kaye bayan sauya shekar Ronaldo.
Kusan dai za a iya cewa wasan zai zama ma'aunin kwazon kowanne Club ba tare da tauraronsa ba, ko da dai dama Madrid na ci gaba da shan kaye bayan sauya shekar Ronaldo. JOSEP LAGO / AFP

A karon farko cikin fiye da shekaru 10 za a fafata a wasan El classico tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar Lahadi mai zuwa ba tare da Ronaldo ko Messi ba.Kusan dai za a iya cewa wasan zai zama ma'aunin kwazon kowanne Club ba tare da tauraronsa ba, ko da dai dama Madrid na ci gaba da shan kaye bayan sauya shekar Ronaldo.

Talla

Rabon dai da kungiyoyin biyu su fafata ba tare da wadannan zakakuran ‘yan wasa ba tun a shekarar 2007 wato kafin zuwansu kungiyoyin biyu masu dabi da juna.

Wasan na Classico na zuwa ne a dai dai lokacin da kociyan Madrid Julen Lopetegui ke ci gaba da shan suka game da rashin nasarar Madrid a kusan wasanni 5 da ta fafata duk kuwa da matsayinta na mai rike da kambun zakarun Turai.

Kididdiga dai ta nuna cewa Madrid ta buga wasa na tsawon sa’o’i 8 da minti 1 ba tare da ta zura kwallo bas ai a wasan ranar Talata inda ta dan yi rawar gani wajen zura kwallaye biyu a ragar Viktoria Plazen ko da dai Victoria ta kusa farkewa gab da karkare wasa inda aka tashi ci 2 da 1.

Ka zalika wasan na ranar Lahadi zai zo a dai dai lokacin da abokiyar dabinta kuma Barcelona ke ci gaba da bayar da mamaki duk kuwa da rashin Kaftin dinta Lionel Messi wanda yanzu haka ya ke jinya bayan samun rauni a hannu, Yanzu haka dai Barcelonar ce ke saman teburin Laliga da maki 18.

Sai dai ana ganin rashin nasarar Madrid a wasan na ranar Lahadi zai iya kawo karshen wa’adin Lopetugei mai shekaru 52 a Bernabeu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.