wasanni

Mamallakin Leicester City ya mutu a hatsarin jirgi

Vichai Srivaddhanaprabha, mamallakin Leicester City
Vichai Srivaddhanaprabha, mamallakin Leicester City REUTERS/Jorge Silva

Mamallakin Kungiyar Kwallon kafa ta Leicester City, Vichai Srivaddhanaprabha ya gamu da ajalinsa bayan jirginsa mai saukar ungulu ya yi hatsari a kusa da filin wasa na King Power.

Talla

Matukin jirgin da wasu jami’an kungiyar biyu har da wani fasinja guda duk sun rasa rayukansu a wannan mummunan hatsarin da ya auku a ranar Asabar.

Jirgin mallakin attajirin ya kama da wuta bayan aukuwar hatsarin, yayin da jami’an tsaro ke cewa babu wani mutum daban daga waje da hatsarin ya shafa.

Mr. Srivaddhanaprabha mai shekaru 60 da haihuwa, ya saye Leicester City ne a shekarar 2010 akan Pam miliyan 39.

Kungiyar ta lashe kofin firimiyar Ingila a shekarar 2016 a karkashin shugabancinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.