Wasanni

Real Madrid na gaf da bayyana sabon kocinta

Mai horar da kungiyar Real Madrid Julen Lopetegui.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Julen Lopetegui. REUTERS/Albert Gea

Kafafen yada labaran Spain sun rawaito cewa kowane lokaci daga yanzu shugaban Real Madrid Florentino Perez zai iya sanar da korar kocin kungiyar Julen Lopetegui, biyo bayan lallasa su da Barcelona ta yi da kwallaye 5-1 a wasan La Liga na wannan Lahadi.

Talla

A halin yanzu dai Real Madrid tana matsayi na 9 ne a gasar La Liga ta Spain maki bakwai tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Barcelona.

Kungiyar ta tsinci kanta a wannan mawuyacin hali ne bayan da Lopetegui ya gaza jagorantarta wajen samun nasarar da take bukata a farkon wannan kakar wasa; kungiyar ta samu nasara kawai ne a wasanni 4 da ta buga, ta yi kunnen doki sau 2, yayin da kuma tayi rashin nasara a wasanni 4.

Lopetegui ya kafa Tarihin zama mai horarwa na farko da Real Madrid ta sha mummunan kaye a karshen bayan soma kakar wasa cikin shekaru 70.

A halin da ake ciki, mataimakin mai horar da Real Madrid Santiago Solari ne ake sa ran zai jagoranci wasan da kungiyar za ta buga na Copa del Rey da kungiyar Melilla cikin tsakiyar wanna mako.

Kafofin yada labaran Spain sun kuma rawaito cewa akwai kakkarfan yakinin cewa, nan bada daewa ba tsohon kocin Chelsea Antonio Conte zai karbi horar da kungiyar ta Real Madrid, in da zai jagoranci wasan La Liga da za ta karbi bakuncin Valladolid a gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.