Wasanni

Ronaldo bayyana ainahin dalilinsa na rabuwa da Real Madrid

Tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo, tare da tsohon mai horar da kungiyar Zinedine Zidane, a lokacin da aka karramasu da da kyautar Ballon d'Or zama gwarzaye kan fannoninsu (na horarwa da kuma kwarewa a fagen fafata wasa).
Tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo, tare da tsohon mai horar da kungiyar Zinedine Zidane, a lokacin da aka karramasu da da kyautar Ballon d'Or zama gwarzaye kan fannoninsu (na horarwa da kuma kwarewa a fagen fafata wasa). Ben STANSALL / AFP

Cristiano Ronaldo ya ce babban dalilinsa na rabuwa da Real Madrid zuwa kungiyar Juventus shi ne fahimtar da yayi cewa, shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez ba ya ganin kimarsa, kamar yadda yake yi a baya.

Talla

Ronaldo ya bayyana haka ne a ganawar da yayi da wata mujallar wasanni ta kasar Faransa, inda ya kara da cewa, bayaga shugaban na Real Madrid wasu daga cikin mambobin kungiyar ma sun daina daukarsa da muhimmanci.

Ronaldo ya ce, ya soma fuskantar rashin bashi kima a Real Madrid bayan shafe shekaru 5 da komawa cikinta bayan rabuwa da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United.

Yayin hirar da Mujallar wasannin, dan wasan na Juventus ya kara da cewa ajiye aikin horar da Real Madrid da mai horar da shi Zinaden Zidane yayi, ya kara masa kwarin gwiwar rabuwa da kungiyar, domin gwada sa’arsa a wata.

A watan Yulin da ya gabata Ronaldo ya koma Juventus kan kudi euro miliyan 100, bayan shafe shekaru 9 yana hasakawa a Real Madrid.

Tun bayan zartas da matakin rabuwa da Real Madrid da Cristiano Ronaldo yayi, har yanzu kungiyar ta gaza samun dan wasan da zai maye gurbinsa wajen ci mata kwallaye a wasannin da take fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.