Wasanni

FA ta ci tarar kocin Chelsea saboda tsokanar United

Mataimakin kocin Chelsea Marco Lanni yayin murnar kwallon da suka rama a wasan da suka tashi 2-2 da Manchester United.
Mataimakin kocin Chelsea Marco Lanni yayin murnar kwallon da suka rama a wasan da suka tashi 2-2 da Manchester United. CheapGoals

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta tilastawa mataimakin mai horar da Chelsea Marco Lanni biyan tarar euro dubu 6, saboda samunsa da laifin nuna murna ta tsokana da ban haushi a wasan da suka fafata da kungiyar Manchester United.

Talla

Lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Oktoba nan, yayin wasan gasar Premier da kungiyoyin biyu suka fafata wanda aka tashi 2-2.

To Marco Lanni yayi tsokanar ce bayan da Chelsea ta rama kwallo ta biyu a ragar United cikin minti na 96, inda kocin ya je gaban bencin kungiyar yana ihu, lamarin da ya baiwa mai horar da United Mourinho haushi ya kuma maida martani.

Tuni dai Lanni ya amsa laifinsa, wanda ya ce bayan kammala wasan ya nemi afuwar kocin United Mourinho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.