Wasanni

An yi barazanar hallaka Zaha dangane da wasan Arsenal

Dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha.
Dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha. REUTERS/David Klein

Dan Crystal Palace Wilfried Zaha, ya ce an aike masa da sakwannin batanci, hadi da na barazanar hallaka shi, a dalilin sanadin samawa kungiyarsa damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, da ya basu damar jefa kwallo ta 2 a ragar Arsenal.

Talla

Zaha ya samo damar ce bayanda Granite Xhaka tade shi a cikin yadi na 16, yayin wasan gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar da ta gabata, hakan ya baiwa dan wasan Crystal Palace Luka Milivojevic damar jefa kwallon a wasan da suka tashi 2-2.

Sai dai Zaha ya ce baya rike da kowa a zuci dangane da barazanar kisan da ake masa, illa ma fatan alkhairi ga masu nufinsa da sharri.

Kididdiga masu bibiyar kwallo ta nuna cewa, tun daga kakar wasa ta 2014/2015, dan wasan Leicester City Jamie Vardy ne kawai yafi Zaha yawan samawa kungiyarsa damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ya samar da damar har sau 13 yayinda Zaha ke da 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.