Wasanni

An gudanar da Jana'izar Shugaban Leicester City

Mutane dake zaman makoki a ofishin Klob din Leicester City don mutuwar shugaban Klob din
Mutane dake zaman makoki a ofishin Klob din Leicester City don mutuwar shugaban Klob din © Reuters

Rahotanni daga birnin Bangkok na Thailand na cewa yau Asabar ake binne gawan hamshakin attajirin nan kuma mai Klob din kwallon kafa na Leicester City Vichai Srivadhanaprabha wanda ya yi hadarin jirgin sama dan tsakanin nan .

Talla

Dan shekaru 60 yayi hadarin ne a cikin jirgin saman sa makon jiya jim kadan da tashin jirgin saman daga kusa da filin wasan kwallon kafa na Klob din na sa.

Da shagon saida kayayyaki daya ya fara harkan kasuwancinsa, kafin ya shahara ya zama kasaitaccen miloniya.

Marigayi Vichai yayi amfani da ribar da yake samu a kamfanoninsa har ya mallaki Klob din Leicester City kuma ya taimakawa Klob din har ta sami nasarar cin kofin Turai a shekara ta 2016

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.