Matsalar da ta hana Kano Pillars lashe kofin Aiteo a Najeriya

Sauti 10:19
Ana sukan tawagar Kano Pillars kan rashin nuna karsashi a wasu muhimman wasanni da ta yi a baya-bayan nan
Ana sukan tawagar Kano Pillars kan rashin nuna karsashi a wasu muhimman wasanni da ta yi a baya-bayan nan kanopillars.com

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne game da matsalar da ta haddasa kashin da Kano Pillars ta sha a hannun Enugu Rangers a wasan karshe na gasar cin kofin kalubale ko kuma Aiteo Cup a Najeriya. Kano Pillars ce ta fara zura kwallaye uku, sannan ta ci gaba da jan ragama har fiye da minti 70. Sai dai abin mamaki, cikin kasa da minti 20 Enugu Rangers ta farke dukkanin kwallayen uku kafin daga bisani ta kuma doke Pillars a bugun fanariti da ci 4-2. Ana kallon wannan nasarar tamkar al'mara, yayin da Pillars din ta kori daukacin 'yan wasanta har sai ta neme su nan gana a cewarta.