Wasanni

Messi da Ronaldo ba za su samu kyautar Ballon d'Or ba - Mbappe

Dan wasan kungiyar PSG, Kylian Mbappé.
Dan wasan kungiyar PSG, Kylian Mbappé. Jean-Paul Pelissier/Reuters

Matashin dan wasa Kylian Mbappe, ya ce har yanzu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne kan gaba a fagen kwallon kafa, sai dai su kwana da sanin cewa, bajintar da ya nuna yayin gasar cin kofin duniya a Rasha, za ta iya bashi damar lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya ta Ballon d’Or.

Talla

Mbappe mai shekaru 19 ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasarar lashe kofin duniya da Faransa ta yi, inda ya ci mata kwallaye 4, lamarin ya bashi damar lashe kyautar mafi kwarewa da kwazon matashin dan wasa a gasar ta bana.

Zalika a kakar wasan da ta gabata, Mbappe ya zama mafi yawan kwallaye a gasar Ligue 1 ta Faransa, inda ya ciwa kungiyarsa Paris Saint Germain kwallaye 11.

Matashin dan wasan dai ya kafa Tarihin zama na biyu mafi karancin shekaru da ya ci kwallaye a babbar gasar kwallon kafa ta duniya, bayan Pele da ya soma kafa Tarihin a shekarar 1958 a lokacin da yake da shekaru 17.

Har yanzu dai babu dan wasan da ya kai Ronaldo da Messi yawan lashe kyautar gwarzon dan kwallon na duniya ta Ballon d’Or, inda kowannensu yake kyautar guda biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI