Wasanni

Monaco ta samu nasarar farko a karkashin jagorancin Henry

Mai horar da kungiyar Monaco Thierry Henry.
Mai horar da kungiyar Monaco Thierry Henry. REUTERS

Thierry Henry ya samu nasarar farko a gasar Ligue 1 ta Faransa tun bayan karbar jagorancin horar da kungiyar Manoco kimanin makwanni 6 da suka gabata.

Talla

A ranar Asabar din da ta gabata Monaco ta samu nasara kan Cean da 1-0.

Sai dai duk da nasarar, tsugunno bata karewa kungiyar ta Monaco ba, kasancewar har yanzu tana ajin ‘yan dagaji da maki 10 a mtsayin ta 19.

A ranar 11 ga watan Agustan da ya gabata, Henry ya soma horar da Monaco, wandanda zuwa yanzu suka rashin nasara a wasanni 4, canjaras a guda 2 sai kuma wannan nasara ta farko da suka samu kan kungiyar Cean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI