Wasanni

Tilas Hazard ya yanke shawara kan zamansa a Chelsea - Sarri

Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Eden Hazard.
Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Eden Hazard. Action Images via Reuters/Lee Smith

Mai horar da kungiyar Chealsea Maurizio Sarri, ya ce tilas nan da gajeren lokaci, dan wasansa na gaba, Eden Hazard ya yanke shawara kan ci gaba da zama a kungiyar, ta hanyar sa hannu kan kara wa’adin yarjejeniyarsa ko akasin haka.

Talla

Lokacin da ya ragewa yarjejeniyar Hazard mai shekaru 27 da Chelsea shi ne daga yanzu zuwa shekarar 2020, a dai dai lokacin da ake ci gaba da alakanta dan wasan da sauyin sheka zuwa kungiyar Real Madrid.

A halin yanzu dai Chelsea na biyan Hazard albashin Fam dubu 350, kwatankwacin dala dubu 450 ne a mako guda.

Dan wasan da kungiyar Chelsea ta saya daga Lille a shekarar 2012 kan fam miliyan 32, ya dade yana bayyana cewa har yanzu yana nazari kan komawa Real Madrid ko kuma ci gaba da zamanza a Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI