Wasanni

Bama neman agajin kowa kan gasar kwallon kafa a 2022 - Qatar

Taswirar filin wasa na Al-Wakrah da Qatar ke kammala yiwa kwaskwarima a birnin Doha, daya daga cikin filayen da za'a fafata wasannin gasar cin kofin duniya ta 2022 a cikinsa.
Taswirar filin wasa na Al-Wakrah da Qatar ke kammala yiwa kwaskwarima a birnin Doha, daya daga cikin filayen da za'a fafata wasannin gasar cin kofin duniya ta 2022 a cikinsa. Reuters

Qatar ta musanta rahotannin cewa tana tattaunawa da wasu kasashe makwabtanta dangane da yiwuwar hada gwiwa domin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.

Talla

Shugaban kwamitin dake lura da shirin Qatar na daukar nauyin gasar Nasser al-Khater, ya ce duk da cewa shugaban FIFA Gianni Infantino na fatan soma aiwatar da sauyin kara yawan kasashen da za su halarci gasar ta 2022 daga 32 zuwa 48, babu gaskiya cikin rahoton suna neman tallafin wasu kasashe.

Sai dai Infantino ya ce muddin karin yawan kasashen ya tabbata, hakan na nufin cewa za’a fafata wasanni 80 a gasar, sabanin 64 da hudu da ake yi a baya, dan haka dole makwabtan Qatar su karbi bakuncin wasu wasannin.

Gwamnatin Qatar ta ce tana kashe akalla dala miliyan 500 a kowane mako guda, kan gine-ginen da za’a yi amfani da su yayin karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar a 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.