Wasanni

FIFA ta rabawa kungiyoyin kwallon kafa dala miliyan 209

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, tare da shugaban Rasha Vladimir Putin yayin wani taro a birnin Moscow. 13/6/2018.
Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, tare da shugaban Rasha Vladimir Putin yayin wani taro a birnin Moscow. 13/6/2018. Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta sanar da biyan wani alawus na musamman da ya kai dala miliyan 209, ga kungiyoyin kwallafar da suka baiwa ‘yan wasansu damar wakilatar kasashen a gasar cin kofin duniya ta bana da aka yi a Rasha.

Talla

FIFA ta ce kungiyoyin kwallon kafa 416 daga kasashe 63 ne, suka amfana da kudaden.

Kowanne dan wasa daga cikin jimillar 736 da suka halarci gasar cin kofin duniyar dai, zai samu kason alawus na dala dubu 8,530.

Kungiyoyin nahiyar turai ne suka samu kaso mafi tsoka na dala miliyan 158 daga cikin dala miliyan 209 da FIFA ta bayar, kuma kungiyar Manchester City ke kan gaba a tsakaninsu da ta samu dala miliyan biyar da doriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.