Wasanni

PSG ta musanta shirin saida 'yan wasanta masu tsada

'Yan wasa biyu mafi tsada a duniya dake kungiyar PSG, Neymar da Kylian Mbappé.
'Yan wasa biyu mafi tsada a duniya dake kungiyar PSG, Neymar da Kylian Mbappé. REUTERS/Christian Hartmann

Kungiyar Paris Saint-Germain ta soki rahoton jaridar L’Equipe ta Faransa, wanda cikinsa ta wallafa cewa, kungiyar ta PSG na shirin sayar da daya daga cikin ‘yan wasanta masu tsada Neymar ko Kylian Mbappe.

Talla

Jaridar ta L’ Equipe ta rawaito cewa, PSG na kokarin daukar matakin ne domin kaucewa saba ka’idar hukumar UEFA, wadda ta haramtawa kungiyoyin nahiyar turai kashe makudan kudi wajen sayen ‘yan wasa fiye da ribar da suke samu.

Sai dai kungiyar ta PSG ta musanta rahoton, inda ta ce, bata saba kowace ka’ida ba, dan haka babu daya daga cikin manyan ‘yan wasanta da za ta saida.

A shekarar 2017, PSG ta sayi Neymar kan euro miliyan 200 har da doriya, farashin dan wasa mafi tsada a duniya, yayinda ta sayi Mbappe daga Monaco kan euro miliyan 166, farashi na biyu mafi tsada a tarihi, bayan da dan wasan ya shafe shekara guda tare da ita a matsayin aro.

Martanin na PSG na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu rahotannin ke cewa kungiyar na shirin kashe euro miliyan 75 wajen sayen Frenkie de Jong, dan wasan tsakiya daga kungiyar Ajax.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI