Wasanni

Robben zai kawo karshen zamansa a Bayern Munich

Arjen Robben na kungiyar Bayern Munich.
Arjen Robben na kungiyar Bayern Munich. REUTERS/Kai Pfaffenbach

Arjen Robben ya bada tabbacin cewa zai rabu da kungiyarsa ta Bayern Munich a watan Juni mai zuwa, lokacin da yarjejeniyarsa za ta kare.

Talla

Robben wanda zai cika shekaru 35 a watan Janairu mai zuwa, ya samu damar bugawa Bayern Munich wasanni biyu ba, saboda raunin da ya samu a cinya, wanda ya warke a yanzu.

Dan wasan zai samu damar bugawa kungiyar tasa wasan gasar zakarun turai na ranar Laraba da za su yi tattaki domin fafatawa da Ajax a birnin Amsterdam.

Robben tsohon dan wasan kasarsa ta Holland ya soma bugawa Munich kwallo a shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.