Wasanni

Henry na fuskantar kalubale a Monaco

Mai horar da kungiyar AS Monaco Thierry Henry.
Mai horar da kungiyar AS Monaco Thierry Henry. REUTERS

Har yanzu sabon mai horar da Monaco Thiery Henry na ci gaba da fuskantar kalubale a gasar League 1 ta Faransa, biyo bayan kayen da suka sha da kwallaye 2-0 a hannun Guingamp a ranar Asabar ta karshen mako.

Talla

Monaco wadda ta kasance zakarar gasar ta League 1 a Faransa a kakar wasa ta 2017, a yanzu tana kan matsayi na 19 da maki 13 kacal bayan buga wasanni 18 a gasar ta Faransa.

Yayin da yake tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki, kocin nasu kuma tsohon dan wasan Arsenal Theiry Henry, ya ce kalubalen da ke fuskantar su ba ya bashi damar hutawa, zalika gajeren hutun Kirsimeti da na karshen shekara zai yi su ne cikin zulumi.

Sai dai da alama kungiyar ta Monaco na ci gaba da yi wa sabon kocin na ta Henry uzuri, la’akari da cewa, shugaban kugiyar Vadim Vasilyev ya ce za su tabbatar cewa sun sayi kwararrun ‘yan wasa a kasuwarsu da za ta bude a watan Janairu da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI