wasanni

Liverpool ta yi zarra, Manchester United ta sake bajinta

Mohamed Salah na ci gaba da taimakwa Liverpool wajen ci mata kwallaye
Mohamed Salah na ci gaba da taimakwa Liverpool wajen ci mata kwallaye REUTERS/Andrew Yates

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta tsawaita jan ragamarta a teburin gasar firimiyar Ingila da tazarar maki shida bayan ta doke Newcastle da ci 4-0 , yayin da Manchester City ta sha kashi a hannun Leicester City da kwallaye 2-1.

Talla

Yanzu haka Liverpool na da tabbacin cewa, za ta shiga sabuwar shekara mai kamawa a dai dai lokacin da ta dare saman teburin gasar.

Dejan Lovren da Mohamed Salah da Xherdan Shaqiri da kuma Fabinho, sune suka jefa kwallayen hudu a ragar Newcastle.

A bangaren Manchester City kuwa, a karo na biyu kenan a jere da take shan kashi, abin da ya mayar da ita a matsayi na uku a teburin gasar, yayin da Tottenham ta dare matsayi na biyu.

A ranar Asabar da ta gabata, Crystal Palace ta doke Manchester City din ta ci 3-2, yayin da tarihi ke nuna cewa, a karon farko kenan tun shekarar 2016 da kungiyar ke shan kashi sau biyu a jere a gasar firimiyar Ingila.

Shi kuwa Eden Hazard na Chelsea ya shiga cikin jerin ‘yan wasan da suka ci wa kungiyar kwallaye fiye da 100 a dukkanin wasannin da suka buka mata.

Dan wasan shi ne ya jefa kwallaye biyu da suka ba su nasara akan Watford da ta jefa kwallo guda a fafatawar da suka yi a ranar Laraba a firmiyar Ingila.

Yanzu haka shi ne mutun na 10 daga cikin jerin ‘yan wasan da suka taba ci wa Chelsea kwallaye fiye da 100, in da yake da kwallaye 101.

Ita ma dai Manchester United ta ci gaba da nuna bajinta tun bayan sallamar tsohon kocinta Jose Mourinho, in da ta samu nasara sau biyu a jere a wasannin da ta buga a baya-bayan nan karkashin sabon kocinta na rikon kwarya, Ole Gunnar Solksjaer.

Paul Pogba ya jefa kwallaye biyu a fafatawar da suka doke Huddersfield da ci 3-1 a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI