Wasanni

Pogba na da hazakar da bai cancanci zama a benci ba- Solskjaer

Dan wasan Faransa da ke taka leda a Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Faransa da ke taka leda a Manchester United Paul Pogba. FBL-ENG-PR-MAN CITY-MAN UTD Manchester United's French midfield

Sabon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya yi ikirarin cewa yanzu dan wasan tsakiya na Club din Paul Pogba ya dawo da hazakarsa ta zura kwallo yayinda yake cike da farin ciki a kungiyar bayan gushewar tsohon kocinsa Jose Mourinho.

Talla

Pogba wanda a baya suka yi ta takun saka tsakaninsa da Jose Mourinho wadda ta kai ga ajje shi a benci a wasanni da dama, ko a was an jiya Laraba shi ne ya zura kwallaye 2 cikin kwallaye 3 da Club din ya zura a ragar Huddersfield a wasan da suka yi nasara da kwallaye 3 da 1.

Haka zalika Solskjaer ya ce Pogba ya taimaka wajen zura kwallaye biyu a wasan sabon kocin na farko da suka yi nasara kan Cardiff da kwallaye 5 da 1.

A cewar manajan wanda ya karbi ragamar horar da United na wucin gadi da kafar dama, Pogba na da hazakar da bai kamata a rika ajje shi a benci kamar yadda Mourinho ke yi ba.

Yanzu haka dai Pogba ya taka leda a ilahirin wasanni 4 da Solskjaer ya jagoranta kuma anga irin bajintar da yak e nunawa wajen kai Club din ga nasara wanda yanzu haka ya ke matsayin na 6 da maki 32 bayan doka wasanni 19 a gasar Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI