Wasanni

Ronaldo ya musanta nuna bakin ciki da bai wa Modric Ballon d'Or

Dan wasan Portugal da ke taka leda a Juventus Cristiano Ronaldo ya mayar da martini ga kalaman zakaran kwallon duniya na bana Luka Modric game da kin halartarsa bikin bashi kyautar Ballon d’Or cikin watan jiya da ya gudana a Faransa, inda ya ce ko kadan hakan baya nuna ya na bakin cikin bayar da kyautar ga Luka.

A cewar Ronaldo mai shekaru 33 ko a lokacin da ya lashe kyautar a shekarun da suka gabata bai sa rai ba, haka zalika a wannan karon ma, don haka bai ga dalilin nuna bakin cikinsa ba.
A cewar Ronaldo mai shekaru 33 ko a lokacin da ya lashe kyautar a shekarun da suka gabata bai sa rai ba, haka zalika a wannan karon ma, don haka bai ga dalilin nuna bakin cikinsa ba. Goal.com
Talla

A tattaunawarsa da manema labarai, Ronaldo ya ce bayan karbar makamanciyar kyautar har sau biyar a tarihin rayuwarsa bai ga dalilin da zai sa ya yiwa Modric bakin ciki ba.

Ronaldo dai ya kauracewa bikin karrama zakaran dan wasa na duniya da na dan wasa mafi hazaka da hukumomin FIFA da UEFA suka karrama Modric, dalilin da ya sanya Modric nuna bacin ransa kan yadda zakakuran ‘yan wasa biyu ciki har da Ronaldon da kuma Messi na Argentina kiri-kiri suka ki bai wa bikin muhimmanci.

A cewar Modric ko da Ronaldo da Messi basu halarci bikin don tayashi murna ba, kamata ya yi su halarta don martaba hukomomin da suka shirya bikin.

Sai dai Ronaldo ya nanata cewa ko kadan rashin halartar ta sa baya da alaka da nuna bakin ciki ko bacin rai game da kin bashi kyautar domin kuwa ko a baya ma bai sa rai ba kuma ya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI