Wasanni

Liverpool na tunkarar babban kalubale a Firimiya

Yanzu haka dai Liverpool din ita ke matsayin ta 1 a teburin na Firimiya sai dai tazarar maki 4 kacal tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Yanzu haka dai Liverpool din ita ke matsayin ta 1 a teburin na Firimiya sai dai tazarar maki 4 kacal tsakaninta da Manchester City ta biyu. REUTERS/Peter Nicholls

Wani rahoton masana wasanni na nuni da cewa tazarar da ke tsakanin Jagora a gasar Firimiya Liverpool da kuma Manchester City shi ne mafi karantar tazara da aka taba fuskanta cikin shekaru 20 tsakanin jagora da mai bi mata baya bayan doka wasanni 21, batun da rahoton ke cewa abu ne mai wuya Liverpool ta iya cika burinta na dage kofin wanda rabonta da shi tun a 1990.

Talla

Rahoton ya ce hazakar da kungiyoyi 4 na saman teburi ke nunawa alamu na cewa kowacce daga cikinsu za ta iya dage kofin dai dai lokacin da ya rage musu wasanni 17 su karkare gasar

Ilahirin kungiyoyin hudu da suka hadar da Liverpool Mancity Tottenham da kuma Chelsea na da tazarar maki 10 ne kacal tsakaninsu sbanin tadda aka saba samu a baya na akalla tazarar maki 12 tsakanin jagora da mai bi mata baya musamman a irin wannan lokaci da aka kai rabin gasar.

Haka zalika rahoton ya bayyana gasar Firimiya ta bana a wadda kungiyoyi basu samu wadataccen maki ba musamman maki 10 da Huddersfield ke da shi wanda shi ne mafi kankanta da wata kungiya ta samu a kakar wasa 11 bayan doka wasa 21.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI