Wasanni

Ramsey na shirin zama dan wasa na biyu mafi tsada a Juventus

Tun a shekarar 2008 ne Ramsey ya kulla kwantiragi da Arsenal kan yuro miliyan 8 da dari 8 daga Cardiff City inda ya zura kwallaye 62 a wasanni 354.
Tun a shekarar 2008 ne Ramsey ya kulla kwantiragi da Arsenal kan yuro miliyan 8 da dari 8 daga Cardiff City inda ya zura kwallaye 62 a wasanni 354. REUTERS

Kungiyar kwallon kafar Juventus ta Italiya ta ce ta na shirye -shiryen kammala sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey wanda kwantiraginsa ya kare da Arsenal din cikin wannan kaka kuma Club din ya gaza cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasan a watan Satumban bara.

Talla

Matukar dai cinikin ya tabbata zai kawo karshen shekaru 10 da Ramsey ya yi a Arsenal yayinda zai zamo dan wasa na biyu mafi karbar albashi a Juventus bayan Cristiano Ronaldo da ke karbar dala dubu 179 kowanne mako.

Yanzu haka dai Juventus ta sanar da yuro miliyan 6 da rabi a matsayin farashin da za ta sayi dan wasan, yayinda kungiyoyin Turai irinsu Bayern Munich Real Madrid PSG da ma Intermilan ke zawarcinsa.

Tun a shekarar 2008 ne Ramsey ya kulla kwantiragi da Arsenal kan yuro miliyan 8 da dari 8 daga Cardiff City inda ya zura kwallaye 62 a wasanni 354 da ya bugawa Arsenal yayinda ya yi nasarar dage kofin FA a shekarun 2014 da 2015 da kuma 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI