Wasanni

Bayern Munich ta nemi adalci a dakatarwar UEFA kan Mueller

Club din ya ce ko da dakatarwar za ta yi amfani bai kamata ta zamo a ilahirin wasanninsu biyu da Liverpool ba.
Club din ya ce ko da dakatarwar za ta yi amfani bai kamata ta zamo a ilahirin wasanninsu biyu da Liverpool ba. © REUTERS/Michaela Rehle TPX IMAGES OF THE DAY

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta ce za ta daukaka kara kan dakatarwar wasanni biyu karkashin gasar cin kofin zakarun Turai da aka yi wa dan wasanta Thomas Mueller.

Talla

Dakatarwar kan Mueller dan Jamus mai shekaru 29 na nuni da cewa ba zai samu taka leda a wasanni biyu na zagayen kungiyoyin 16 da Munich din za ta faffata da Liverpool ba.

Tun a wasan karshe na zagayen rukuni rukuni ne UEFA ta fitar da Mueller daga filin wasa bayan bashi jan kati a wasan wanda aka yi canjaras tsakanin Munich da Ajax kwallaye 3 da 3 kafin daga bisani ta sanar da dakatar da shi daga buga wasanni biyu bayan tabbatar da cewa da gayya ya hankade tare da dukan dan wasan gaba na Ajax Nicolas Tagliafico.

Sai dai Club din ya ce ko da dakatarwar za ta yi amfani bai kamata ta zamo a ilahirin wasanninsu biyu da Liverpool ba, wasan da lallai suna bukatar nasara don tsallakawa mataki na gaba.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne dai Bayern Munich za ta yi tattaki zuwa Anfield kafin daga bisani ita ma Liverpool ta je Allianz Arena a ranar 13 ga watan Maris.

A cewar Club din ya na fata ko da Mueller bai samu wasan da za su yi tattaki zuwa Liverpool ba amma ya zama ya samu zarafin taka leda a wasan da Liverpool za ta zo musu har gida cikin watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI