Wasanni

Gwagwarmayar gasar firimiyar Ingila a bana

Sauti 10:23
Liverpool ce ke jan ragama a teburin gasar firimiyar Ingila
Liverpool ce ke jan ragama a teburin gasar firimiyar Ingila Paul Childs/Reuters

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan gwagwarmayar kungiyoyi a gasar firimiyar Ingila ta bana, in da tuni Liverpool ta dare saman teburi da maki 60, abin da ya bai wa magoya bayanta kwarin guiwar cewa, za su lashe kofin gasar a wannan karo bayan shafe tsawon shekaru 29 ba tare da daukan kofin ba. Kazalika kungiyoyi na ci gaba da fafutukar ganin sun kare a matakin 'yan hudun saman teburi, yayin da wasu kuma ke kokarin ganin ba su kammala ba a matakin 'yan dagaji.