Turai

Masu bincike na kokarin gano tarkacen jirgin dake dauke da Emiliano Sala

Wasu daga cikin magoya bayan Emiliano Sala a Nantes dake kasar  Faransa
Wasu daga cikin magoya bayan Emiliano Sala a Nantes dake kasar Faransa REUTERS/Stephane Mahe

Bayan bacewar jirgin dake dauke da sabon dan wasan Cardif Emilliano Sala dake kan hanyar sa ta komawa da sabuwar kungiyar sa, jama’a da dama ne yanzu haka daga Faransa zuwa Ingila ke ci gaba da bayyana alhinin su.

Talla

Jaridu na Turai sun bayyana cewa dan wasan ya aike da sako ta kaffar manhaja ta Watsapp, inda yake cewa ya na cikin fargaba ganin halin da jirgin dake dauke da su yake ciki.

Dan wasan mai shekaru 28 ya na mai cewa akwai alamar jirgin dake dauke da su zai fadi, ya karasa da cewa nan da sa’oi daya da rabbi indan babu duri’ar su, ba shi sa zaton za a samo su ko kuma gano inda suka shiga.

Ga duk alamu masu bincike zasu ci gaba da gudanar da bincike don gano yankin da jirgin ya shiga.

Wasu daga cikin fittatun yan wasa, Maradonna da Ronaldo,wadanan yan wasa sun aike da sakwonnin su zuwa iyalan dan wasa, tareda sa ran za a gano inda dan wasan yake yanzu haka.

Kulob na Cardiff a ingila ya yi cinikin dan wasan ne a kan kudi milyan 17 na Euros daga kungiyar Nantes ta kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI