Wasanni

Manchester City za ta iya lashe kofuna 4 a wannan kaka - Guardiola

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola REUTERS/Phil Noble

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce abin alfahari ne ya zamana Club din ya yi nasarar lashe kofuna har 4 cikin kaka guda dai dai lokacin da ya ke shirin komawa wasannin cin kofin FA bayan takaitaccen hutu.

Talla

City dai ita ce kungiya daya tilo da ta ke da zarafin iya lashe kofunan Firimiya da FA da kofin League da kuma zakarun Turai la’akari da matakin da ta ke a kowacce gasa.

Yanzu haka dai City na da tazarar maki 4 ne kacal tsakaninta da Liverpool da ke saman Teburi, a bangare guda kuma an ga rawar da ta ke takawa a gasar ta FA da ma yadda ta ke shirin tunkarar wasan karshe a gasar League tsakaninta da Chelsea cikin watan Fabarairu baya ga gasar zakarun Turai.

A gobe asabar ne Manchester City za ta kara da Burnley a zagaye na 4 na wasannin cin kofin FA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.