Isa ga babban shafi
Wasanni

Portugal za ta kwace lambar yabo mafi girma da ta baiwa Ronaldo

Cristiano Ronaldo, yayin wasan kusa da na karshe da suka fafata da Wales, a gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai na shekarar 2016.
Cristiano Ronaldo, yayin wasan kusa da na karshe da suka fafata da Wales, a gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai na shekarar 2016. REUTERS/Kai Pfaffenbach Livepic
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa, ya ce gwamnatinsa tana nazari kan yiwuwar kwace babbar lambar yabo da ta baiwa dan wasan kasar Cristiano Ronaldo.

Talla

Matakin a cewar shugaba Rebelo de Sousa, na da nasaba da hukuncin biyan tara da kotun Spain ta yanke kan Ronaldo, bayan samunsa da laifin kin biyan haraji, yayin da yake wasa a kungiyar Real Madrid.

A shekarar 2016 Portugal ta karrama Ronaldo da lambar yabo mafi girma da ake baiwa farar hula ta ‘Portuguese Order of Merit’ a turance, bayan taimakawa kasar da ya yi, wajen lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai.

Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, wata kotun Spain ta yanke hukuncin tilasatawa Cristiano Ronaldo biyan Dala miliyan 3 da dubu 57 saboda kin biyan makudan kudade na haraji ga gwamnatin kasar.

Da fari hukuncin kan Ronoldo na daurin shekaru 2 biyu ne a gidan Yari amma aka sassauta hukuncin zuwa biyan tarar euro dubu 365 na take, tare da biyan karin euro miliyan 3 da dubu 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.