Wasanni

Kocin AS Roma ya musanta shirin ajiye aikinsa

Mai horar da kungiyar AS Roma Eusebio Di Francesco.
Mai horar da kungiyar AS Roma Eusebio Di Francesco. REUTERS/Alessandro Bianchi

Mai horar da kungiyar AS Roma, Eusebio Di Francesco, ya ce ko kadan baya tunanin ajiye aikinsa, sakamakon lallasa su da Fiorenntina ta yi da kwallaye 7-1, a zagayen kwata final na gasar cin kofin Italiya a ranar Laraba.

Talla

Yayin zantawa da manema labarai bayan wasan, Di Francesco ya ce tabbas kungiyar tasa ta gaza, to sai dai abinda kawai zai iya shi ne neman afuwar magoya baya da hukumar gudanarwa kungiyar ta AS Roma.

Kayen da Roma ta sha a hannun Fiorentina, ya zo ne kwanaki uku, bayan da ta rasa damar komawa matakin kungiyoyi hudun farko a gasar Seria A, yayin fafatawar ta da kungiyar Atalanta.

Duk da cewa AS Roma ce da fari ta soma jefa kwallaye uku a ragar Atlanta, daga bisani ta yi sakaci Atlanta ta rama kwallayen kuma aka kammala wasan na Seria A 3-3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.