Wasanni

An soma gasar tseren gudun yada kanin wani a Legas

Wasu dake fafatawa a gasar tseren gudun yada kanin wani da bankin Access ke shiryawa a Legas.
Wasu dake fafatawa a gasar tseren gudun yada kanin wani da bankin Access ke shiryawa a Legas. The Nation

An soma gasar tseren gudun yada kanin wani a safiyar yau Adabar a Legas, daga babban filin wasa na jihar da ke Surulere.

Talla

Karo na hudu kenan da bankin Access da ke Najeriya ke shirya gasar da gudun na kilomita 42, wadda ke samun halartar dubban masu tseren gudu daga kasashe da dama.

Wanda ya lashe yayi nasarar lashe gasar tseren yada kanin wanin daga bangaren bakin zai samu kyautar dala dubu 50, na biyu zai dafe kyautar dala dubu 40, yayinda na uku zai samu kyautar dala dubu 30.

Sai dai a bangaren ‘yan Najeriya da ke gida, wanda yayi nasarar zuwa na farko zai lashe kyautar naira miliyan 3, na biyu naira miliyan 2, yayinda na ukunsu zai samu naira miliyan 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI