Wasanni

Najeriya ta ci gaba da rike matsayinta na 4 a Afrika - FIFA

Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland.
Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files

Najeriya ta ci gaba da rike matsayinta na hudu a fagen iya kwallon kafa a nahiyar Afrika, sai dai a matakin duniya ta fuskanci koma baya kadan, inda ta rasa matsayinta na 44 da mataki biyu, wato a yanzu ta koma ta 46.

Talla

Wannan na kunshe cikin rahoton da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitawarwa duk wata kan kwarewar kasashen duniya a fagen taka leda, wanda hukumar ta FIFA ta fitar a yau Alhamis.

FIFA ta kuma bayyana cewa, Qatar koma matsayi na 55 a matakin kwarewar fafata kwallo a duniya daga tsohon matsayinta na 93.

Wannan dai ita ce nasara mafi girma da kasar Qatar ta samu a fagen kwallon kafa tun bayan wadda ta gani a shekarar 1993.

A nahiyar Afrika, FIFA ta ce Senegal ta fi kowace kasa kwarewa a fagen iya kwallo, biye da ita Tunisia ce sai kuma Morocco a matsayi na 3, yayinda Najeriya ke matsayi na 4.

Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, Ghana da Kamaru na kan matsayi na 5,6, da kuma 7, yayinda Masar, Burkina Faso da Mali ke kan matsayi na 8, 9 da kuma na 10.

A mataki na duniya kuwa, Belgium ta ci gaba da rike matsayinta na daya, Faransa na biye da ita a matsayi na biyu, Brazil ta uku, sai kuma Croatia da Ingila a matsayi na hudu da na biyar 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.