Wasanni

Ramsey ya amince da yarjejeniyar komawa Juventus

Aaron Ramsey.
Aaron Ramsey. AFP

Dan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey ya sa hannu kan yarjejeniyar komawa kungiyar Juventus tsawon shekaru hudu.

Talla

Ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa Ramsey zai isa birnin Turin domin soma haskawa sabuwar kungiyar tasa, la’akari da cewa, sai a 30 ga watan Yuni, yarjejeniyarsa da Arsenal za ta kare.

A Karkashin yarjejeniyar da ya cimma da Juventus, kungiyar za ta rika biyan Ramsey Fam dubu 400 a kowane mako.

Ramsey ya fara kwallonsa ta matakin kwararru ne da kungiyar Cardiff City a shekarar 2007, daga bisani kuma ya koma Arsenal a watan Yulin 2008.

Cikin shekaru 11 da ya shafe tare da Arsenal, ya bugawa kungiyar wasanni 256, ya ci mata kwallaye 38, tare da shi kuma ta lashe kofin FA 3, na Community Shield 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.