Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta shiga tsaka mai wuya

Dan wasan Kylian Mbappe, yayin zura kwallo ta 2 a ragar Manchester United.
Dan wasan Kylian Mbappe, yayin zura kwallo ta 2 a ragar Manchester United. REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Manchester United na fuskantar kalubalen rasa damar kaiwa zagayen kwata final a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bana.

Talla

Kalubalen ya biyo bayan rashin nasarar da suka yi a filin wasansu na Old Trafford, yayin wasan da suka fafata na ranar Talata, wanda PSG ta samu nasara da kwallaye 2-0.

PSG ta jefa duka kwallaye biyun a ragar United bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, ta hannun ‘yan wasanta Presnel Kimpembe da Kylian Mbappe.

Wani karin kalubale da United ka iya fuskanta shi ne rashin dan wasanta na tsakiya Paul Pogba a wasanta na gaba da kungiyar ta PSG, kasancewar a ba zai samu damar buga wasan ba, saboda jan katin da alkalin wasa ya bashi, bayan karbar katunan dorawa 2.

A ranar 6 da watan Maris, Manchester United za ta yi tattaki zuwa Paris don fafatawa da PSG zagaye na biyu a gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.