Wasanni

Za a soma amfani da fasahar VAR a gasar AFCON

Fasahar VAR, mai taimakawa alkalain wasa da maimaicin bidiyo.
Fasahar VAR, mai taimakawa alkalain wasa da maimaicin bidiyo. REUTERS/Javier Barbancho

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF, ta amince da shirin soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da maimaicin bidiyo VAR, a gasar cin kofin nahiyar ta Afrika AFCON, a wannan shekara.

Talla

CAF ta yanke shawarar ce a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, da ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika ajin matasa ‘yan kasa da shekaru 20.

Karo na farko kenan da za a fara amfani da fasahar ta VAR a gasar cin kofin nahiyar Afrika, wadda za a soma daga ranar 19 ga watan Yuni, zuwa 21 ga watan Yuli na 2019.

Hukumar CAF ta taba gwajin yin amfani da fasahar ta taimakawa alkalin wasa da maimaicin bidiyo, a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a shekarar 2018, tsakanin kungiyar Al Ahly ta Masar da kuma Esperence ta Tunisia.

Fasahar VAR ta karbu ne bayan soma amfani da ita a gasar cin kofin duniya ta 2018 da Rasha ta karbi bakunci, hakan yasa a halin yanzu hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA ta kaddamar da amfani da fasahar a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.