Wasanni

Mahaifin Neymar ya musanta tuntubar Barcelona kan dansa

Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar.
Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar. AFP

Mahaifin dan wasan gaba na PSG Neymar, wato Neymar Santos, ya musanta rahotannin da ke cewa, yayi kokarin tuntubar Barcelona domin dan wasan ya sake komawa tsohuwar kungiyar tasa.

Talla

A watan Agustan 2017 Neymar ya sauya sheka daga Barcelona zuwa Paris Saint-Germain kan euro miliyan 222, sai dai tun a waccan lokacin, bai dade da sauyin shekar ba, aka soma rade raden zai koma tsohuwar kungiyar tasa.

A cewar Mahaifin Neymar, wato Neymar Santos, ba zai yiwu a rasa samun rahotannin yiwuwar komawar dansa zuwa wasu manyan kungiyoyi ba, la'akari da cewa babban dan wasa ne, amma batun kokarin komawa Barcelona ba gaskiya bane.

A halin yanzu Neymar yana ci gaba da jiyyar raunin da ya samu a kafarsa, yayin wasan PSG da Starsbourg na gasar cin kofin Faransa a karshen watan Janairu, wanda likitoci suka suka ce zai shafe makwanni goma kafin komawa fagen wasa.

Neymar wanda ya ci wa PSG kwallaye 20 a dukkanin wasannin da ya buga mata a kakar wasa ta bana, ya sake samun rauni ne a kafar da ya taba samun karaya cikin watan Fabarairu na shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.