Wasanni

Manchester City ta lallasa Schalke 04

Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling bayan jefa kwallo ta 3 a ragar Schalke 04.
Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling bayan jefa kwallo ta 3 a ragar Schalke 04. Reuters

Kungiyar Manchester City ta nuna bajinta yayin fafatawar ta da Schalke 04 a gasar ta Zakarun Turai, inda ta samu nasara da kwallaye 3-2.

Talla

Da fari Manchester City sai da ta fuskanci shan kaye muraran a zagayen farko na wasan matakin kungiyoyi 16 a gasar ta zakarun Turai, inda Schalke 04 ke jagorantarta da 2-1, kafin daga bisani ta yi namijin kokarin rama kwallayen da aka jefa mata.

‘Yan wasan City da suka hada da Sergio Aguero, Sane da kuma Sterling suka jefa kwallayen uku, yayinda Nabil Bentaleb ya ci wa Schalke 04 kwallayenta 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.