Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya ci kwallo sau uku a wasa 1 karo na 50

Lionel Messi, dan wasan gaba na Barcelona.
Lionel Messi, dan wasan gaba na Barcelona. Reuters/John Sibley Livepic
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi ya samu nasarar cin kwallaye uku cikin wasa daya karo na 50, a tarihinsa na murza leda, abinda ake kira da hat-trick.

Talla

Messi ya samu nasarar ce a wasan gasar La Liga da suka lallasa Sevilla da kwallaye 4-2.

A zagayen farko na wasan Sevilla ce ta jagoranci Barcelona da kwallaye 2-1, kafin daga bisani Messi ya rama tare da karin guda biyu.

A jimalace Messi ya jefawa Sevilla kwallaye 36 kenan a wasanni 35 da suka fafata tsakaninsu da Barcelona a matakin gasar La Liga, Copa del Rey, da sauran wasannin da suka taba haduwa.

A yanzu Barcelona ke jagorantar gasar La Liga da maki 57, Atletico Madrid na biye da maki 50, sai kuma Real Madrid mai maki 48 a matsayina uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.