Wasanni

Yadda rauni ke dakile yunkurin ‘yan wasa na kafa tarihi a duniyar kwallo

Sauti 10:08
Dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint-Germain, Neymar, lokacin da ya samu rauni a kafarsa yayin fafatawa da Marseille ranar 25 ga watan Fabarairu na 2018.
Dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint-Germain, Neymar, lokacin da ya samu rauni a kafarsa yayin fafatawa da Marseille ranar 25 ga watan Fabarairu na 2018. Reuters/Stephane Mahe

Shirin na wannan makon da AbduRahman Gambo Ahmad ya jagoranta, ya dora ne akan na makon jiya, wanda yayi nazari kan yadda masu horar da kwallon kafa ke fuskantar kalubale, da kuma yadda matsalar rauni ke kashe yunkurin ‘yan wasa na kafa tarihi a duniyar tamaula.Shirin ya kuma tuntubi masana kan yadda Barcelona ke lallasa Real Madrid a yanzu.