Wasanni

Real Madrid ta yi barin kofuna 3 cikin mako 1

Kocin Real Madrid, Santiago Solari ya ce ba zai karaya ba a kokarinsa na cimma nasarori duk da kalubalen da suke fuskanta.

Mai horar da kungiyar Real Madrid Santiago Solari.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Santiago Solari. AFP/JAVIER SORIANO
Talla

Solari ya sha alwashin ne, yayin tsokaci kan wasan gasar zakarun Turai da kungiyar Ajax ta lallasa Real Madri da kwallaye 4-1 a filin was anta na Santiago Bernabeau, lamarin da ya sa kungiyar ta Madrid ficewa daga gasar ta bana, la’akari da cewa a zagayen farko ta samu nasara kan Ajax ne da kwallaye 2-1 a Holland.

Solari ya kuma jaddada cewa ba zai yi murabus ba, duk da mummunan kayen da ta sha a hannun kungiyar ta Ajax, wanda shi ne kaye na uku a jere da Real Madrid ke fuskanta a cikin mako guda, biyu daga cikin kayen kuma ta sha su ne a filin wasanta.

Karon farko kenan cikin kusan shekaru 10 da Madrid ke gaza kaiwa zagayen kwata final a gasar zakarun Turai.

Hakan na nufin Real Madrid rikito daga gasar Copa del Rey, bata kuma da damar lashe kofin La Liga, ga shi kuma ta fita daga gasar zakarun Turai duk cikin kwanaki bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI