wasanni

Zidane ya yi watsi da tayin Real Madrid

Zidane ya lasha wa Real Madrid Gasar Zakarun Turai sau uku a jere
Zidane ya lasha wa Real Madrid Gasar Zakarun Turai sau uku a jere REUTERS/Andrew Boyers

Zinedine Zidane ya yi watsi da damar sake komawa Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid don ci gaba da horar da ita kamar yadda tsohon shugaban kungiyar, Ramon Calderon ya bayyana.

Talla

A wata zantawa ta wayar tarho, Zidane ya shaida wa shugaban Real Madrid, wato Florentino Perez cewa, ba zai dawo kungiyar a yanzu ba bayan ya bukaci dawowarsa.

Sai dai ya nuna alamar watakila ya sake karbar aikin horarwa da kungiyar a cikin watan Yuni.

Zidane ya raba gari da Real Madrid ne a kakar da ta gabata, kwanaki biyar da lashe mata kofin Gasar Zakarun Turai karo na uku a jere.

Ana saran Real Madrid ta yi gagarumin garanbawul saboda yadda ta gamu da matsalolin rashin nasara a bana, yayinda Ajax ta yi waje da ita daga Gasar Zakarun Turai karkashin Santiago Solari da ake ganin kungiyar za ta sallame shi nan kusa.

A bangare guda, rahotanni sun nuna cewa, da yiwuwar kungiyar ta maye gurbin Solari da Jose Mourinho wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2013 da nufin komawa Chelsea da aikin horarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.